Muhabbatil Qalb written By Asmy B. Aliyu



Posted byAiHausa Novel
Price300
CategoryHausa Ebooks
Uploaded On07 Feb, 2023
Upload Time8:29 am
Hits218 Views
Author

Asmy B. Aliyu

Writer Group

Writer Associat

Novel Genre

CommentNo Comments

Muhabbatil Qalb Written By Asmy B. Aliyu

Drivern gidan su na danno hancin motar cikin babban compound É—in gidan mai É—auke da sashe har guda uku ta buÉ—e ido da mamaki take kallon motar Maina saraki dake fake acikin babban compound. Kara buÉ—e ido tayi tana kallon motar yaushe yazo? ta tambayi zuciyarta bayan ko minti talatin basuyi ba da gama waya dashi. Kai tsaye ta fice daga cikin motar, sashen dake can Æ™arshe ta nufa da gudu duk da yayda ta kwaso zafin rana ga yunwa  da take ji haka ta nufi entrance É—in shiga part É—in. Door bell ta danna ba'a É—auki lokaci ba mai aiki tazo ta buÉ—e mata, ganin Hafsat yasa ta ba ta hanya tana gaisheta, bata ko kulata ba ta shige, kai tsaye stairs ta nufa tana haÉ—awa da gudu. ÆŠakinsa ta nufa dake É“angaren dama da sauri ta buÉ—e Æ™ofar dai-dai lokacin Muhammad Maina ya buÉ—e Æ™ofar toilet ya fito jikinsa É—aure da babban towel fari sol. Da gudu taje ta Æ™anÆ™ameshi tana yi masa ihu. ware manyan eye's É—insa yayi masu kama da na cat yana kallonta, da wata kalan murya yake  faÉ—in. "Sweet zaki kada mufa." Ta maÆ™e kafaÉ—a tana turo baki ta wani haÉ—e rai lokaci É—aya ya riga da yasan laifinsa bai faÉ—a mata zuwansa ba. Komawa tayi kan soofa ta zauna ranta a É“ace ta tallabe fuskarta da hannayenta duka biyu. Hakan da tayi yasa Maina Saraki sakin wani irin kayattacen murmushi, hannayensa ya haÉ—e duka biyu da ido yake bata hakuri.

 MaÆ™e kafaÉ—a tayi alamar bazatayi ba, ya cije lips. Warware towel É—in ya shiga yi ta fiddo da dukkan idonta da gudu ta nufi Æ™ofa ya bita da kallo still da wani irin murmushi cikin fuskarsa. Har ta sauka Æ™asa babu kowa cikin parlorn. Wani irin murmushi ne kwance cikin fuskarta, tana Æ™aunar Maina Saraki da dukkan zuciya da ruhinta. Kai tsaye part É—in su ta nufa. Mama ce a parlorn tana shirya lunch Asma'a ce zaune akan rug tana bitar karatunta na hadda. Dakyar Hafsat Saraki ta gaisheda Mama da suka  haÉ—a ido da haka ta nufi part É—in su, Asma'a ta taÉ“e baki ta cigaba da abunda takeyi, Mama ta Æ™araso cikin parlorn tana faÉ—in. "Kije ki É—ibi abinci lokaci na tafiya kin san Shantima bai son jira nasan kuma shi zai kaiku Islamiyya tunda driver tare da Baffan ku zasu fita." Daga haka Mama ta nufi stairs Asma'a ta turo baki tana faÉ—in. "Mama nifa bana son jelop rice dan Allah nayi wainar fulawa mana?" Wani kallo Mama keyi mata tana faÉ—in. "Har yaushe kikayi wainar kuka tafi islamiya?" Da sauri Asma'a ke cewa. "Minti nawa ne Mama? dan Allah." Ta faÉ—a mata cikin sanyi murya, Mama ta girgiza kai tana cigaba da tafiya take faÉ—in. "Ni dai babu ruwana saboda kin san halin wanda zai kaiku islamiyyar." Kwashe books É—inta tayi tabi bayan Mama. Kusan biyu da rabi ta fito daga parlorn ta nufi part É—in Ummah, Hafsat ce kawai a parlorn tana waya, kallo É—aya Hafsat tayi mata ta cigaba da wayarta, kai tsaye É—akinsu Ikraam ta nufa kusan cin karo sukayi da Ikraam É—in itama ta fito cikin nata shirin islamiyyar uniform É—in kalar light blue da hijab har Æ™asa. "Ziyada baza taje ba ne? Yah Shantima zai kaimu fa." Ikraam ta taÉ“e baki tana faÉ—in. "Wai kanta ne yake ciwo, kuma nasan karya take Ita dai bata iya hadda bane kawai." ÆŠaga kafaÉ—a Asma'a tayi, tare suka sauka har Æ™asa Ikraam ta Æ™araso cikin parlorn tana kallon Hafsat wacce har lokacin waya takeyi. "Addah Hafsat ki bani alkawarin É—ari biyar É—in da kikayi min." Hafsat ta kalleta tace.
 "Kije É—akina kan mirror dressing ki É—auka, É—ari biyar kawai zaki dauka na gaya miki." Daga haka Ikraam ta juya ta nufi É—akin Hafsat Saraki wanda daman Asma'a ta daÉ—e da barin parlorn tana fitowa compound ta hango Yah Shantima da Maina Saraki suna tahowa. "Mugun gidan su ya dawo kenan?." Zuciyarta ta faÉ—a tamkar Asma'a bata so ta gaishesu dukkan su. Shantima kawai ne ya karÉ“i gaisuwarta amma Maina Saraki ya nufi part É—in Inna. Da harara ta bishi tana jin wani É“acin rai tace. "I hate him with passion." Ta faÉ—a tana wani binsa da wata hararar. Shantima Saraki ya kalleta yana faÉ—in. "Ina sauran kuma?" Zatayi magana sai ga Ikraam ta fito, da mamaki yake faÉ—in. "Ziyada fa?" Ikraam ta buÉ—e hannuwa tana faÉ—in. "Tace wai kanta na ciwo." A fusace Shantima ya nufi sashensu yana kwalawa Ziyada kira tun daga kofar parlor. Asmaa ta girgiza kai tana faÉ—in. "Nidai wallahi zai saka muyi latti." Ta faÉ—a tamkar zatayi kuka. Ƙarasawa sukayi wurin motar Shantima Saraki suna jiran fitowarsa. Fuska babu walwala yayi tsaye a Æ™ofar É—akin yana bin Ziyada da mugun kallo, Ya kalli agogon rolex É—in dake É—aure cikin damtsen hannunsa yake faÉ—in. "Na baki minti goma kacal Ziyada Saraki ki fito, ko sakan É—aya kika Æ™ara wallahi haÉ—uwar mu ba zai yi miki kyau ba." Da haka Shantima Saraki ya bar room É—in wanda kusan cin karo sukayi da Ummah, É—auke kai yayi ya wuce. Tsaye tayi bakin Æ™ofar tana kallon yadda hawaye suka cika fuskar Ziyada tana saka uniform ummah ke faÉ—in. "Shi wannan mai yazo ya faÉ—a maki?" Cikin fashewa da kuka take faÉ—in. "Yace minti goma ya bani na saka uniform na fito mu tafi, kuma wallahi Ummah yau malam Aminu kasheni zaiyi saboda ban iya haddar da aka bani ba, kuma fa Ummah kusan shafi huÉ—u ake bina ko na wancan satin ban bayar ba." Cikin wani yanayi Umma ke cewa. "Shi uban kine da zai sakaki zuwa makarantar? Kiyi zamanki babu inda zakije." Ziyada na girgiza kai take faÉ—in. "Ni dai bari naje Ummah haka kawai ya zaneni a banza kuma naje islamiyya a kara zaneni." Da haka tabi gefen uwar ta wuce. Baki Ummah ta saki tana kallon Ziyada dake tafiya cikin mugun sauri. Rai a É“ace Ummah ke faÉ—in. "Bari uban naku ya dawo ni dai a yiwa Æ´aÆ´ana  iyaka da Shantima tunda bashi ya haifa min ba." Hafsat ta girgiza kai tana faÉ—in. "Toh meye laifinsa anan Ummah? daman kin san halin Ziyada bata son karatu." Ummah zatayi magana Hafsat ta miÆ™e tsaye ta nufi Æ™ofa wacce kananun kayane ajikinta wanda suka kamata sosai sai É—an Æ™aramin veil da tayi rolling tana faÉ—in. "Zanje mu gaisa da Inna da safe ban shiga ba." Wani kallo uwar ta riqa yi mata har ta fice daga parlorn. Tun a Æ™ofar parlorn shiga take jin hirar Inna, takalmin da ta gani a Æ™ofar parlorn ya tabbatar mata da Maina ya shigo ciki. Tsaye tayi a bakin Æ™ofar tasan halin Inna yanzu zata ce sabida taga Maina yazo ne shi yasa ta kwaso jiki tazo itama." Abunda taji Innar na faÉ—a yasa ta kasa shiga cikin parlorn, wani irin faÉ—uwa gabanta yayi. "Ai Æ™ara a haÉ—e aurenku kai da Shantima a huta, toh me ake jira idan taje É—akin kawai ba sai tayi karatun ba. Ace kaninka zaiyi aure ba tareda naka ba? ai da sake gaskiyya naga dai kai auren gida zakayi ba'a waje za'a nemo matar ba, ban san me ake jira ba har yanzu. Idan iyayen nan naku suka cigaba da biyewa bokon nasarar nan ba za'a yishi yanzu ba. Amma ai kaga shi Shantima da yafi ka hankali kaga har an kai kuÉ—in gaisuwa rana kawai suke jira a saka, wai fa dan haka ma na matsawa Kabirun lamba ya kiraka kazo ayi komai a Æ™are."


 Wani irin murmushi yake ya yiwa Inna, baki sake Inna ke kallon sa, ya shafa sumar kansa still wearing a smile, mitsi-mitsi da Ido Inna tayi tana kallonsa, zatayi magana ya rungumeta cikin jikinsa yana sauke wani irin numfashi saboda bai san dame zai sakawa Inna ba, daman kullum Hafsat Idan yace ayi aure sai ta kawo masa uzurin karatunta, shi kuma baya son abunda zai É“ata ran Hafsat Saraki dan yana yi mata soyayyar da shi kansa bai san adadinta ba. kullum azumin Litinin da Alhamis baya wucesa akan Allah ya mallaka masa Hafsat Saraki dukan ta. Bai taÉ“a sawa ransa abubuwa zasu zo haka cikin sauqi ba. Yanzu idan su Baffa da Inna suka yanke hukunci yasan ba zata yi jayayya ba, haka kuma bazata É—auka da saka hannunsa acikin lamarin ba. Da baya -baya take barin part É—in Inna tana jin idonta na rufewa, tafiya kurum take ba tare da ta san inda take saka Æ™afafunta ba. Tana son Maina Saraki da dukkan zuciya da gangar jikinta. Sai dai idan kuma sukayi aure zai rabata da Besty É—inta data zamar mata rabin jiki.


 Cikin Æ™anÆ™ani lokaci wani irin zazzabi ya rufe Hafsat. Kai tsaye part É—in su Hafsat Maina ya nufa daman bai shiga ba, da Mama suka fara gaisawa da fara'a take faÉ—in. "Yaushe a gari?" Ya shafa sumar kansa yana faÉ—in. "ÆŠazu na shigo Mama Abba fa?" Ya tambaya yana sakin murmushi. "Bai dawo daga kasuwa ba." Mama ta tambayeshi ya aiki ya faÉ—a mata "Alhamdulillahi." Tayi masa tayin abincin rana ya faÉ—a mata Alhamdulillahi ya koshi, da haka ya shiga part É—in Ummah itama da fara'a ta tarbesa tana yi masa sannu da zuwa. A nan kuma take tambayarsa zuwa babu sanarwa? yana shafa sumar kansa yake faÉ—in. "Wallahi kuwa ai ba daÉ—ewa zaiyi ba. Mai aiki Ummah ta saka ta kawo masa ruwa da snacks ya faÉ—a mata a koshe yake. "Abban ku yana kasuwa sai zuwa anjima zakaga ya shigo." Maina yace. "Haka Mama take gaya min." Yana jin kunyar ya tambayi Ummah Hafsat da haka yayiwa Ummah sallama. Har ya kai Æ™ofa take faÉ—a masa Hafsat tana bacci itama bata daÉ—e da dawowa daga makaranta ba." Yace." "Anjima ai zan dawo gaisheda Abba." Da murmushi Ummah tayi masa fatan sauka lafiya sannan ta faÉ—a masa ya gaisheda Hajiarsu. Kai tsaye É—akin Hafsat ta nufa ta sameta a kwance, ta kira sunanta daga bakin Æ™ofa, É—agowa tayi tana kallon Ummah lokaci É—aya Ummah ta zaro ido tana Æ™arasowa cikin É—akin cike da tashin hankalin take faÉ—in. "Meya samu idonki?" Tamkar jira take ai mata magana, kawai Hafsat Saraki ta fashe da kuka. Da tashin hankali Ummah ta wani daka mata tsawa tana faÉ—in. "Wai uban me akayi maki ne?" Cikin kukan take faÉ—awa Ummah hirar da taji Maina Saraki nayi da kakar su, baki wangale Ummah ke kallonta tana cewa. "Ban taba sanin ke shashasha bace sai yau Hafsat, Abunda zakiyi murna sai kuma ki fara kuka?" Cikin ihun kuka Hafsat ke faÉ—in. "Karatuna fa Ummah? kin san idan auren nan ya tabbata Yah Maina zai iya saka a É—aukeni daga nan a mai dani Sokoto, ni kuma bana son karatu a Sokoto na fison  anan, ni dai ban shirya aure yanzu ba saboda duk friend's É—ina ba wacce tayi aure yanzu saini." Tagumi Ummah tayi da mugun mamaki tana kallon Æ´artata, ba tare da Ummah ta Æ™ara magana ba tabar mata É—akin. Tana ganin yadda Maina Saraki ke faman kiranta a waya amma ta share kiran taki dagawa......

Domin Sauke Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!


Download

Click the below button to download, pls in case you get trouble trying to download kindly drop a comment.


Download any type of hausa novel which include Hausa Love, Adventure, fiction, Fantasy and other genre Hausa Novel paid and free and read them in confort of your zone at ArewaBooks.Com


 



Author’s Contact

  • Name : Asma'u B. Aliyu
  • Wattpad Handle : @ Asmy B. Aliyu
  • Nick Name : Asmy B. Aliyu
  • Whatsapp Number : 
  • Nationality : Nigeria
  • Email :
  • Group : Writers Association

The Book is not free