HIRA DA MATATTU ..2 (TRUE STORY)
Na tsaya cak ina makerketa na ji a raina kawai in fasa zuwa ganin alqalin da na zo gani. Yayana ne ya yi min hanyar ganinsa tun ba yau muke fama ba sai yau Allah Ya yi.
Muryar yayana na ji yana daka min tsawa akan in zo mu je, mutumin na ta jiranmu ya karaso tun dazu. Shiyasa ma ya ce fara yin gaba saboda in fara koro bayanai kafin ya iso.
Na bi shi a baya ina rawar dari, ina shiga ofishin ko zama ban yi ba na hango Sharifa ta gifta da sauri, sai na zabura na daka tsall, na sake daga labule na leqa ta.
Wallahi babu tantama ita ce kuma wannan ofishin da muka fito dazu ta shi ta shiga.
Wannan karon ba firgita kadai na yi ba zatuwa ce. Yayana ya kai kololuwar jin haushina kamar ya mare ni ya rufe ni da fada yayin da dattijon alkali ma ya qule.
Kara zan shigar muka zo neman shawara a wajensa akan shariar pre order kaya da na lunkuba kudaden mutane na turawa wata amma babu kudi babu kaya.
Amma wallahi gaba daya da aka tambaye ni lissafin da yadda aka yi tun da farko na manta komai.
Ba su sallame ni ba na fice da sauri na nufi ofishin da Sharifah ta shiga. A bude yake ban yi wata-wata ba na fada ciki, dan na ga mutane na ta shiga su na fitowa.
Abin mamaki ba wancan dattijon ba ne wani matsayi ne a zaune akan kujerar kusa da shi.
Na daga hannuna mai karkarwa ina nuna kujerarar, na tambaya, na ce " me waccan kujerar shima ya mutu ko?"
Aka hau kallon-kallo a tsakanina da su. Yayin da suka fara jeho min tambayoyi me nake cewa? Me make so? Wa nake nema?
Na hau kame-kame suka gaji suka koro ni waje, ina fita na ci karo da yayana ya dire kwandon masifa da zagi akaina. Yana cewa na kunyata shi gobe ma rana ce kada in sake cewa ina neman taimakonsa idan na dauko rigima.
Mu ka dunguma hanyar get ni dai ban tanka masa ba, amma kowa ya ganni ya ga kwantacciya.
"Innalilahi wa inna ilaihi rajuun" ya ji na ambata a gigice na nufi bakin get da gudu ina kiran Sharifa, Sharifah. Ita na hango ta tare adaidaita zata Shiga. Ta waiwayo ta dube ni sannan ta shiga.
Yayana ya zabura ya damqo ni ya na cewa "ke yaya haka ne? Wacece Sharifah kuma?"
Na ce masa ya rabu da ni adaidaita zan hau. Ya ce ai da mota muka zo.
Kwalla kiranta nake amma bata waiwayo ba ta shige adaidaita ta tafi ta bar ni. Yayana ya Amince na yi gamo shigowata cikin kotu, daman ga bishiyoyin tsamiya nan.
Ya saka ni a mota yana min tofi. Yayin da ya dauki waya ya kira mahaifiyarmu yana tambaya daman Samha tana da aljanu? Mama ta ce ko kadan ban taba yi ba. Ya ce gamu nan zuwa gidan.
Mu ka tafi, a daidai danja(traffic light) muka tsaya sai ga Sharifah a cikin adaidaita. Na zabura na kwalla sunanta "Sharifah! Sharifah!!" har sai uku ta kalle ni ta dauke kai.
Sai yayana ya fara karatu a bayyane har da gangarawa gefen hanya dan kada in bude qofar mota in fita.
Babu makawa ya tabbatar na yi gamo kuma sunan aljanar Sharifa.
A haka muka isa gida jikina da zazzabi ina karkarwa. Ni ba abin in ce na ga fatalwa ba a sake tabbatarwa da haukata.
Ana ta min addua har sai da zazzabin ya sauka na sami bacci. Abin mamaki sai na yi mafarkin Sharifa da alqalinta su na cewa in zo in tattara ledoji da takardu in share wajen zaa yi baqi.
Na farka da wani mugun tsoro gami da gigita. Allah Ya sa da salati na farka ba da ihu ba.
Nan dai yan gidan suka sake taruwa a kaina ana ta min tofi, yawu kala-kala da me warin goro da na miyar kuka, har da na tabar wiwi dan muna da 'yan shaye-shaye wai su ma agajin addu'a suka kawo min.
Allah mai iko, na fita daga gida lafiya na dawo a zauce.
Ban samu sun bar ni na sarara ba sai da daddare na sami damar kiran kawayenmu daban-daban da muka yi karatu a Jami'a tare, kowacce ta tabbatar min sun jima baxu ji doriyar Sharifa ba amma tabbas da ta mutu da sun ji. Wata daga ciki kuma ta ce ai jiya ma sun yi waya Sharifah na raye. Na ce ta bani lambar ta turo min na kira a kashe. Kuma layin ba mai register ba ne.
Innalilahi wa inna ilaihi rajuun toh maganar wa zan kama? Babbar matsalar ma dai ace dare yayi kowa yayi bacci ya bar ni, fatalwa ta bayyana.
Mijina baya gari dan haka na fada masa a waya, zan kwana a gida saboda yanayin ciwon. Dan an sanar da shi tunda rana. Nan da nan yayi Amanna .
A tsakiyar kannena na kwana bayan na hana su bacci, dakyar dai na samu bacci ya kwashe ni.
Washe gari aka hana ni fita in je gidan su Sharifa in gani, dan ana tunanin bana cikin hayyacina.
Aka karbe wayata dan sun gaji da wayar da nake yi ina ta kiran sunan Sharifa! sharifa.
Na dauko hotunan bikina ina kallonta, ita ta yi min babbar qawa, ga ta nan a hoto ita da kanwarta kamarsu daya kuwa mai suna Shariqah.
Daga cewa zan zagaya bandaki sai na fice ban tsaya a ko ina ba sai a kofar gidan su Sharifah Nasir. Na gamu da wasu yara sai na tambaya ko an yi mutuwa a gidan nan?
Yaro daya ya zabura ya ce min " eh an dade da yi Sharifah ce ta rasu."
Sai daya yaron ya zabura ya ce "ba Sharifah ba ce ta rasu Shariqa ce."
Nan fa musu ya kaure a tsakaninsu. Yayin da na dora hannu aka kamar mai shirin kurma ihu dakyar na daure.
Fitowa Bello Nasir ce daga cikin gidan ta sa na ji sanyi wato kaninsu Sharifah. Na tare shi da sauri na ce " Bello wai Sharifah ta rasu?"
Ya ce "Au Aunty Samha ba ki sani ba ne? Ai an yi shekara da rasuwar Shariqah ba Sharifah ba dai."
Na zabura na ce " a a kai ma ka yi kuskure Sharifah ce ta rasu ba Sharuqa ba."
Sai na ga yayi min wani irin kallo na ai sai ki yi, ya kada kai da sauri ya Shiga mota ya tafi ya bar ni.
Ina tsaye a kofar gidan na kasa Shiga kasancewar na tabbatar uwa da ubansu sun dade da rasuwa kuma Shariqa tana gidan aurenta.
Abin mamaki sai na ga suffar Sharifah a jikin windo tana leqowa. Mun hada ido wallahi ita ce . Sai na tabbatar ni kadai nake ganinta ba sa ganinta .
To be continue
Madalla da ALQALAMIN JUT
0 Comments