"; Wace Ce Ita (Who Is She) Chapter 54 Complete Novel

Wace Ce Ita (Who Is She) Chapter 54 Complete Novel

 

WACE CE ITA⁉️ (WHO IS SHE⁉️)

Unique Barakancy

                             FIFTY-FOUR📍


     “What’s this?”…..

Ya fada batareda ya karanta content din ciki ba…..

    “Result din tests din da aka yiwa fatima da khaleel ne!”….

Abby ya bashi amsa…

 Da mamaki Deen yace;

     “Ya akayi tests ban sani ba? Yaushe akaje hospital? And the last time I checked zahrah bata da lafiya, so yaushe akayi haka ban sani ba?”……

Harararshi mami tayi ganin yanda yake musu magana kamar shi ya tara su a gurin, cikin daure fuska tace;

     “Ai ba dole in zamuyi komai sai an shawarce ka ba, in bazaka karanto mana abinda yake ciki ba miko!”…..

Murmushi Abby yayi yace;

     “Kwantar da hankalinka Saifuddeen, blood sample dinsu na aiko aka karba duka sannan na bawa amintaccen likitana yayi duk binciken daya dace”…..

Sake daure fuska deen yayi ya kalli Abby yace;

     “But what if he gave a fake blood? Abby ya za’ayi ace kawai a bada blood sample? Ai kamata yayi a diba direct kowa yana gani kuma!”….

Daka masa tsawa dad yayi cikin bacin rai yace;

     “Bakada hankaline? How could you even question us like this! Bamusan abinda mukeyi bane? My friend zaka bar shashancin da kakeyi kayi abinda aka saka ko kuwa!”…….

Impulsively suka ga ya mike ya ajye musu takardar ya fita….. 

Da ido suka bishi gabadaya har ya fita daga part din, girgiza kai umm tayi ta dauki paper daya yasar ta shiga duba content din….

Bayanin abinda ke ciki tayi musu wanda duk babu matsala, abu daya ne shima kuma it’s something that can be overlooked, abin shine khaleel SS ne kamar yanda Deen ya fada, sai akaci sa’a ita kuma AA ce, sauran abubuwan kuma duk babu matsala… 

Nan da nan aka tsai da magana aka kuma shaidawa khaleel cewa an bashi fatima officially, khaleel harda kukan farin ciki saboda yanda yake ji kamar an daura auren ne, ga tests din da akayi babu wani problem, shi ko me zai cewa Allah banda godiya…… 

      Direct part dinsa ya wuce yanajin kamar yayi hauka, gani yake kamar babu wanda aka renawa hankali kamar sa, ace sanda aka karbi blood sample kowa ya sani amma banda shi, saboda kuma an rainasa sai a bashi ace shi ya karanto abinda ke ciki bayan yasan komai shiryayye ne, shi ya rasa meyasa suke san hadata da wannan khaleel din kamar babu mazan arziki a duniya, amma ya yiwa kansa alkawari daga rana me kamar ta yau ya fita daga sabgar baby tee har abada!, idan taga dama ta auri uban khaleel ma ba damuwarsa bace….

Sosai ya yiwa kansa fada akan bata precious time dinsa da yake wurin ganin rayuwarta ta inganta duk a banza, har planning din komawa bakin aikinsa yayi, ya bar musu garin gabadaya ma yayi nisa da kowa yayi focusing akan career dinsa, ze bata kidney dinsa kamar yanda yayi niya amma bazasu hada tafiya ba, zeje kawai a cire nasa ya tafi amma tabbas zeyi avoiding duk wani abu daya hada da ita, but the question is can he really do it?!….. 

     “To hell with her! I can do it!”…..

Ya fada yana banging bangon dakin, sai kuma ya zauna a bakin gado ya cigaba da tsara yanda zeyi disappearing…..

Yafi 30mins a zaune yana sakawa  da kwancewa, sam ya kasa tsaida abu daya daya kamata yayi, tuno da yanzu haka suna chan ana maganar auren kawai yaji kansa na juya masa, mikewa tsaye yayi ya fara ball da duk abinda yaci karo dashi, hakan be ishe sa ba ya fara tarwatsa kayan dake kan mirror, haka ya dinga daukan turaruka yana rotsasu a bango ko zeji sanyi a ransa…….

     Mami da umm na zaune bayan su Abby sun tafi harda khaleel daya cewa baby tee ze zo da daddare, sai baby tee dake kwance akan cinyar mami, kawai sukaji sallamar mutane, (Hajiya Laila) mahaifiyar eesha ce a gaba wacce ta kasance kawar mami ta arzi, sai mahaifiyar billy biye da ita, sai eesha data kasance karshen shigowa, idonta yayi ja sosai alamun tasha kuka ba kadan ba…. 

Dago baby tee mami tayi murmushi dauke akan fuskarsu ita da Umm suka hau yi musu sannu da zuwa…. 

     “Hajjaju ashe kina tafe”….

Mami ta fada tana typing message a wayarta….

    “Eh wallahi Justice, Doctor ashe kina gari haryanzu, na dauka kin koma tuntini”….

Murmushi umm tayi tace;

     “Abubuwa ne suka rike ni wallahi, ai da tuni na tafi”….

Gyada kai maman eesha tayi tana kallon baby tee tace;

      “Gaskiya dai, kar dai wannan yar gurinki ce?”…

     “Itace, fatima takwarata ba”..

Mami ta bata amsa tana murmushi…

      “Masha Allah, she has grown up to a very beautiful lady, sai kuma musha biki ko fatima?”…..

Murmushi kawai baby tee tayi batareda tace komai ba……

Saita fuskarta hajiya laila tayi ta kalli eesha data rukube a gefe daya tace;

     “Ita ta taso mu a gaba wai something is happening in this house, meyafaru justice?”…

Umm ce tayi saurin karba da fadin;

      “Au haka akayi? Eesha meya faru toh?”…..

Fashewa da kuka eesha tayi dake masoraciya ce sosai, ta hau basu labarin duk abinda ta sani a game da abinda billy takeyi da yanda billy ta kwallafa rai akan baby tee tin suna hostel amma baby tee bata bada fuska ba, har yau da suka zo gidan billy ta zuba mata abu tasha a drink, sosai ta musu bayanin iya abinda ta sani tsakani da Allah da irin shawarwarin da tasha bawa billy amma bata dauka…….

Tana direwa mamanta ta dauketa da wani lafiyayyen mari, sannan cikin bacin rai tace;

     “Who are you trying to fool da zakice babu ke a ciki? Ai duk wani abu da billy is involved kina ciki! Ba aminyarki bace? I’ll make sure you pay for this tinda baku da hankali!”…..

 Rushewa da kuka eesha tayi kamar zararriya tace;

     “Wallahi mummy ban taba yi ba, ki tambayi kowa, dan Allah kiyi hakuri”…..

Rufe ta da duka tayi tsabar takaici, tasan ba lallai tana yi din ba kamar yanda ta fada, amma ance abokin barawo barawo ne, in kaga mutum yana irin wannan yaushe zaka zama so close da shi in kanada hankali? Wa ze ji maganar nan ya yarda eesha bata ciki bayan amintakar dake tsakaninsu da billy?…..

    (PS; masu abota da mutanen banza kuma kunsan mutanen banza ne toh wallahi ku dena if not it’ll get to a point da bazaku iya defending kanku ba! In kunne yaji jiki ya tsira!)

Rige rigen kwatar eesha daga hannun hajiya laila su umm sukayi suna ta bata hakuri, ita ko mahaifiyar billy na tsaye kamar statue ta rasa abun yi, damuwarta daya yanzu ina billy take kafin tasan matakin da zata dauka…..

     “Dan Allah ku barni in mata tsinannan duka dan Allah! I’m really disappointed in her wallahi!”….

Zaunar da ita mami tayi tace;

     “A’a ba za’ayi haka ba Justice, yanzu ina ita Billyn take?”….

Dakawa eesha tsawa tayi tace;

     “Ba tambayarki akeyi ba?!”….

Cikin shesshekar kuka tace;

     “Tinda yaya saif ya fita da ita banganta ba”….

Harararta mamanta tayi tace;

     “Ai da yasani ya hada dake! Kuma tun wuri zan gayamasa ya rabu dake dan yafi karfin me mugun hali irinki”….

Ai sai eesha ta sake rushewa da kuka kamar tayi hauka, bata taba dana sanin kawance da billy ba sai ranar, ashe umaima tayi gaskiya datace mata wata ran sai billy ta sata a problem, gashi tun ba’ayi nisa ba billy ta rabata da wanda take so, itako ina zatasa ranta taji dadi?……

Umm har zata tura baby tee taje ta kirawo saif wata zuciyar tace gwara taje da kanta duba da yanda yayi ficewarsa dazu, tashi tayi tace musu tana zuwa…. 

Direct part din Deen ta tafi lokacin ana kiran sallar mangariba, murda kofar parlourn tayi tajita a bude, shiga tayi da sallama dauke a bakinta, babu kowa a parlourn sai tashi kamshin turerensa daya hade da sanyin ac, direct bedroom dinsa ta nufa tana jinjina tsafta irin na saif, shi ko masu aiki be yadda su shigo masa part da sunan gyara ba, da kansa yake abunsa…

Tin kafin ta karasa takejin karar fashe fashe, sosai hankalinta ya tashi ta karasa bakin kofar da sauri, knocking ta hau yi zallar mamaki na kara kamata…..

      “Go away!! Just go away! I don’t want to see anyone!”….

Deen ya fada cikin wani irin yanayi mara dadi……

Cikin lallashi tace;

     “Umm dinka ce fa saif! Zo ka bude kofarnan”……

Cikin bacin rai yace;

     “I need space please umm, I’ll see you later!”…

      “Ni kake cewa you need space? Your umm? Open the door and tell me what’s wrong with you, kaji my son?”…..

Jikinsa ne yayi sanyi yaji baze iya kin bude kofar ba, saidai sam bayaso taga yanda yayi messing dakin, amma kuma this is umm din da at all cost bayaso yayi disrespecting…..

A hankali ya bude kofar kadan, tana shirin shiga yayi saurin rigata fitowa, a take ta gane beda gaskiya duba da yanda duk yayi rough, hakan kuma ya tabbatar mata shi yake fashe fashen nan, batayi insisting sai ta shiga ba sai ma ruko hannunsa da tayi suka dawo parlour, zaunar dashi tayi a kusa da ita ta kamo hannunsa cikin wani kalan yanayi tace;

     “When will you stop this bad habit? Shikenan in abu na damunka sai ka hau fasa abubuwa? Who does that for God’s sake? Meyake damunka saif?”…..

Be bata amsar tambayoyinta ba sai ma wata maganar daya sako mata…

     “How is baby tee? Is her waist still paining her? Ta sha maganin dana bata?”…..

Kallonshi kawai take unbelievably, sai kuma ta girgiza kai tace;

     “She’s fine, now tell me your problems?”….

Wani yawu ya hadiye cikin dacin rai yace:

     “Yanzu abinda ake min a gidan nan ana kyautawa umm? Shikenan babu wanda ya daukeni da mahimmaci da za’a yanke abu ba’ayi shawara dani ba?”….

Kada kai umm tayi tana jinjina manyance da san girma irin na Deen, wai ba’ayi shawara dashi ba kamar shine ya haifesu basu suka haifesa ba, murmushi tayi tace;

     “Abinda ya saka fashe fashe kenan?”…..

      “No! Hannuna ne ya bige abu mistakenly”.

     “Yayi kyau”..

Ta fada ba dan ta yarda dashi ba….

     “Yanzu umm sai ki yarda baby tee ta auri wanchan gayen?”…..

Ya jeho mata tambayar daya kasa rikewa….. 

     “Toh ya zanyi tace tana so?”…..

   “Guda nawa baby tee take da har tasan wani soyayya at this young age?”….

Murmusawa tayi tace;

     “Toh ni dai ba abinda ya kawo ni ba kenan, tambayarka inda ka kai yar mutane nazo yi?”…

     “Wa kenan?”…. 

Ya tambaya mamaki dauke akan fuskarsa…..

     “Kawar eesha? Ina ka kaita?”….

Har ga Allah shi ya manta da ita tin bayan ya rufeta a boys quarters, hade rai yayi yace;

     “Bansan inda take ba, I only punished her and let her go”….

Cikin rashin yarda umm tace;

     “Banyarda ba, na fa san halinka saif, ina ka kaita?”……

Kamar bazeyi magana ba sai kuma yace;

      “Bangama punishing dinta ba!”…..

      “Ya isa haka saif, ga mahaifiyarta chan tazo ma, kawai ka fadamin ina ka kaita”…..

     “Gaskiya ku bari gobe umm! Ko baby tee sai da ta kwana a gurin bare wannan yar iskar!”…

     “Ikon Allah ashe har wani gurin gyaran hali ne da kai bamu sani ba, wato baby tee batayi karya ba kenan a abinda ta fada mana?”…. 

Sai a lokacin yayi realizing baran baramar da yayi, amma kuma abinda ya basa mamaki ai sunyi da baby tee bazata fada ba, kenan ta fada musu abinda ya mata?, cikin san gyara zancensa yace;

     “Ba fa yanzu bane, amma me tace muku nayi Umm?”…..

Strictly tace;

     “Kaga tun muna mu biyu ka tashi muje ka fito da yar mutane, wannan bayanin ka yishi daga baya!”….

Shan jinin jikinsa yayi ya mike kamar mara laka ya nufi kofa, girgiza kai kawai umm tayi ta bi bayanshi…… 

Umm batayi mamaki ba ganin sun nufi boys quarters sai ma addu’ar shiriya da take masa aranta, sannan ta kara tabbatar da maganar baby tee da tace ya kulleta a boys quarters….. 


     “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un! Innalillahi wa inna ilaihi raji’un!”…..

Shine kawai abinda umm take maimaitawa tun bayan taci karo da billy dake kwance ko numfashi batayi, juyowa tayi da niyar ta masa na kudinsa, saidai me wayam babu shi babu alamarsa, abinda bata sani ba ma tana shiga ya faki idonta ya fece……

Dialing number mami tayi tace mata tazo yanzu tagani sannan ta kira 911(emergency) na asibitin deen…..

Rankayowa sukayi gaba dayansu harda eesha suka tawo boys quarters…… 

Sosai suma hankalinsu ya tashi ganin ko motsi billy batayi ga jikinta duk shedar bulala alamun tasha duka harda na hauka…..

Fashewa da kuka maman billy tayi ta rungumota tana fadin;

     “Ko menene ya sameki nina jawo miki, idan kika mutu bazan yafe wa kaina ba, shi da ya mata haka shima ban yafe masa ba, Allah ya isa tsakanina da kowa na gidan nan”….

Babu wanda ya tankata ta cigaba da zage zagenta tana kuka…..

Suna cikin wannan hali 911 suka zo, saidai kememe taki yarda su tafi da ita wai kar wanda ya taba mata ya’, suna kallo ta tafi da yarta abinta basu hanata ba…. 

     “Allah ya kyauta! Kinga dai tsatson da kike kawance ko? Ai kingama zaman hostel daga yau, dama abinda yasa kika nacewa zaman hostel kenan ashe”…..

Hajiya laila ta fada tana nuna eesha….

Hakuri eesha tayita bata har lokacin hawaye ya ki dena zuba akan fuskarta, Umm ce tasa baki tace dan Allah abar zancen haka, abinda ya faru ya riga ya faru saidai muce Allah ya kiyaye gaba…..  

Hannun eesha da baby tee Umm ta kamo suka shiga ciki suka bar mami da kawarta suna tattaunawa akan lamarin….. 

       Suna zaune su uku bayan sun idar da sallah, yafito baby tee da hannu Umm tayi, karasowa tayi umm ta nuna mata guri kusa da ita ta zauna tana sunkuyar da kai, hannu ta daura a wuyarta da kanta dan taji yanayin temperature dinta, dago habarta tayi bayan taji komai normal tace;

      “How’re you feeling dear?”…..

A sanyaye tace;

     “I’m okay”….

    “Are you sure? Cikin fa yana miki ciwo haryanzu?”…..

     “Eh kadan amma”….

Gyada kai tayi tace;

      “Mami tasa a miki different food, je kici sai kizo in baki maganin kinji ko?”…

Mikewa tayi tace;

      “Toh”….

Har ta kai bakin kofa umm ta sake dawo da ita..

     “Hey dear!”….

Juyowa tayi tana sauraran abinda zata fada….

     “Are you sure you’re okay? Why’re you so silent?”…..

Umm ta tambaya dan shiru shirun da takeyi yayi yawa, kamar karsu dawo daga asibiti taga duk ta kara yin laushi…..

Murmushi me kyau tayi tace;

      “I’m very okay mom”…..

Gyada kai umm tayi tace;

      “Fine, just make sure kinci abincin sosai, okay?”…..

       “Insha Allah”….

Ta fada tana fita daga dakin…..

Tinda suka fara maganganu eesha take kallonsu, sosai suka bata sha’awa even though itama tana sharing good moment sosai da mom dinta, amma da yake yau tasan me rabata da mummy sai Allah sai take jin kamar baby tee is so lucky da bata da lefi….. 


       “Come here Aisha”….

Ta jiyo muryar umm data koma bakin gado ta zauna ta kirata ba alamun wasa, da sauri ta karasa inda take, umm na nuna mata gefenta ta zauna amma ta kasa kawai ta zauna a kasa hawaye na zuba a idonta tin kafin taji abinda umm zatace……

Dago fuskarta umm tayi tana share mata hawaye tace;

      “Why would you choose to be a homosexual? Ina ganin hankalinki aisha ashe ba haka bane? Ina iliminki da tarbiyyarki yake?”….

Fashewa da kuka eesha tayi tace;

      “Wallahi ni ban tabayi ba, dan Allah ki yarda dani umm, ni ba yar lesbian bace, dan Allah ki taimakeni ki yarda umm”…..

Kallon yanda take kuka umm tayi, tana sane tayi addressing dinta directly saboda ta kara gane gaskiyar lamarin, amma from the look of things eesha gaskiya take fada, still bata nuna mata ta yarda ba tace;

      “Nobody is above mistake and we all are not perfect, ba lallai kowa ya miki uzuri ba amma ni zan miki and I’ll help you overcome it, yanzu inaso ki fadamin tsakaninki da Allah and I promise to help you out, kina ciki ko?!”……

Wani irin fashewa da kuka tayi tace;

      “Wallahi umm ko al-qur’ani kika bani zan dafa, billy ce kawai takeyi, kuma itama ina mata fada, kawai bataji ne, amma wallahi ni ban taba yi ba”…..

          “Then how comes you get so close with someone of such habit, ko fa gidannan zaki zo tare kuke zuwa, why?!”….. 

      “Umm zaman hostel ne yasa muka zama so close, kuma bansan haka take ba sai daga baya, bayan na sani kuma kullum cikin gayamata gaskiya nake”…..

      “And has she ever make an attempt to change?”….

Girgiza kai tayi tana kara dana sanin sanin billy a rayuwarta, babu masifa umm take mata magana amma sai taji har tafi shiga taitayinta akan yanda mamanta ta dinga mata masifa….

Kada kai umm tayi tace;

      “You see! And da kikaga she’s not willing to change what were you supposed to do?”….

A hankali tace;

      “In rabu da ita”….

      “Good! But you didn’t! Kinsan illar abota da mutum irin haka aisha? Abokin barawo barawo ne! Kome zakiyi babu wanda ze yarda batare kuke ba, sannan ba’ace karkayi magana da bad person ba, kawai ya zamana gaisuwa sai kuma nasiha that’s all, amma karki yarda ace kowa ya sanki da mutum irin haka!”…. 

        “Nagane mistake dina umm, kuma bazan sake ba wallahi”.

Eesha ta fada tana shesshekar kuka…. 

Nasiha me ratsa jiki umm tayi mata har saida eesha taji ta tsani billy, sai da umm taga jikinta yayi sanyi sosai sannan tace;

      “Ki kwantar da hankalinki everything will be fine Insha Allah, ki dai kiyaye”….

Jiki a sanyaye tace;

      “Ameen ya Allah, umm dan Allah kice mummy ta barni in kwana anan, wallahi duka na zatayi in muka koma gida, kuma tace sai ta gayawa daddy”….

Dagota umm tayi ta zaunar da ita a gefenta sannan tace;

      “Bazan iya hanata tafiya dake ba aisha because if I’m in her shoes too I would have react the same way or even more, abu daya zan iya shine in roketa karta sake dukanki, daddyn ki kuma nasan ba zata fadamasa ba, ke kuma you should try and convince her ta yarda babu ke a ciki“…..

        “Thank you so much umm, zanyi yanda kikace Insha Allah, nagode sosai”…..

     “You’re welcome dear, tashi kije kici abinci kema”….

Harta mike sai kuma wani abu ya fadomata, dawo wa tayi ta zauna kamar zatayi kuka tace;

       “Umm yanzu shikenan na rasa yaya saif? Wallahi ina sonsa”…. 

Murmusawa umm tayi tace;

       “Baki rasasa ba dear,  ze wuce shima Insha Allah, and I’ll try and convince him too, kema sai ki dage ki masa proving innocence dinki”….. 

Murmushin da tinda aka fara case din eesha batayi ba tayi sannan tace;

      “Nagode sosai umm, I just can’t thank you enough”….

Sai kuma ta marairaice tace;

       “amma kamar baby tee tanajin haushina umm, naga taki kulani tinda abin ya faru, shikenan we can’t be friends?”……

Dan murmushi umm tayi tace;

       “Inji waye? Good friends ma kuwa, kawai bata da lafiya ne, amma in kika sauka yanzu talk to her, you can even explain everything to her too, I know she’ll understand”…..

      “Toh umm, nagode”…..

>>>Also Click Here To Download Complete Book Document

      Tana zaune bayan ta idar da sallahr isha lokacin su eesha basu dade da tafiya ba, kiran wayar khaleel ne ya shigo wayarta, ta dauka tasa a kunne tana murmushi…. 

       “My wife to be!”…..

Khaleel ya fada grinning from ear to ear…

      “Yes darling khal”..

Ta bashi amsa tana murmushi itama…..

      “I’m just so glad baby, I can’t believe an bani ke yau, I just can’t wait akawomin ke gidana as my wife, wifey bazan iya bacci ba ranar, I can’t wait to officially call you wifey, I love you so much baby”…..

     “I love you too honey, nima ina cikin farin ciki sosai”…..

      “Really?”…

Khaleel ya fada smiling broadly….

      “Sosai ma!”….

Ta bashi amsa murmushi ya kasa barin fuskarta, har mamaki abun yake bata yanda lokaci daya yasa taji tana farin ciki, ita da ta yini sai a hankali yau…. 

         “Well I have a surprise for you, I’ll come pick you up by 9pm, can I?”…..

      “Yes darling!”…. 

     “Okay wifey, will call you when I’m coming, byeee”……

        “Byeeeee”….

Ta fada tana kashe wayar, har zata ajye wayar taji karar shigowar text message, budewa tayi duk a tunaninta yan mtn ne, kawai taci karo da sakon daya bata mamaki ya kuma daga mata hankali…..


Domin Sauke Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!

  Thank you all for all the prayers and good wishes, naji sauki sosai yanzu Alhamdulillah❤️

Post a Comment

0 Comments

Ads


Click Here To Download This Book